Jirgin sama makare da maganin Coronaviros ya sauka a Najeriya daga kasar madagascar

Jirgin sama makare da maganin Coronaviros ya sauka a Najeriya daga kasar madagascar

An bayyana cewa katoton jirgin saman Nigeria cike da maganin gargajiya wanda kasar Madagascar ta samar ya sauka a Nigeria, wanda zaa fara gwada amfani dashi akan yan Nigeria da suka kamu da cutar Coronavirus.

Maganin ya temaka wajen kawar da annobar cutar Coronavirus a kasar Madagascar kuma al’ummar kasashe masu yawa na Africa suke ta amfani dashi domin magance cutar Coronavirus.

 Sai dai har yanzu Hukumar lafiya ta duniya WHO bata kai ga amincewa da maganin ba, duk da kasashe na cigaba da jidar maganin zuwa kasashensu

Kasar Nijar dake makotaka da Nigeria tun a satin daya wuce ta karbo maganin daga kasar Madagascar kuma take amfani dashi ga mutanen kasar da suka kamu.

Anan Nigeria ana kyautata zaton za’a fara rarraba maganin zuwa jihohin da annobar Coronavirus tafi tasiri sosai, kafin daga bisani a mika zuwa sauran jihohin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.