MATAN GWAMNONIN AREWA SUN BADA TALLAFI GA MARASA KARFI

MATAN GWAMNONIN AREWA SUN BADA TALLAFI GA MARASA KARFI

Mai Dakin Gwamnan jihar Jigawa Hajiya Magajiya Badaru Abubakar ta kaddamar da shirin bada tallafi na matan gwamnonin arewa ga mata masu karamin karfi.
Da take jawabi a wajen bikin Hajiya Magajiya Badaru Abubakar tace matan gwamnonin arewa ne suka bullo da wannan shiri domin tallafawa mata masu karamin karfi a cikin alumma
Ta kuma bukaci matan da zasu amfana da tallafin da suyi cikakken amfani dashi wajen ciyar da iyalansu.
Hajiya Magajiya Badaru Abubakar ta jaddada kudirin kungiyar matan gwamnonin arewa na bullo da managartan tsare tsare domin tallafawa rayuwar matan yankin arewa.
Mai dakin na gwamnan jihar Jigawa ta kuma yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga mata dasu cigaba da yin addu’o’i domin samun sauki daga cutar corona.
Tun a farkon jawabinta na maraba kwamishiniyar al’amurran mata Hajiya Yelwa Tijjani ta jinjinawa mai dakin gwamnan jihar Hajiya Magajiya Badaru Abubakar bisa hangen nesanta na tallafawa rayuwar matan jihar.
Ta bayyana mai dakin na gwamna a matsayin uwa ta gari mai taimakawa matan jihar.
Sauran wadanda suka yi jawabai sun hadar da mataimakiyar shugabar mata ta jamiyyar APC ta jiha Hajiya Rabi broker da mai dakin mataimakin gwamnan jiha Hajiya Hadiza Umar Namadi.
Daga bisani mai dakin gwamnan ta kaddamar da rabon kayayyakin tare da tallafin mai dakin mataimakin gwamnan jiha Hajiya Hadiza Umar Namadi da mai dakin shugaban KH Dutse Hajia Talatu Yakubu Yargaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.