Sabbin mutane 14 sun kamu da cutar covid-19 a kano
Hukumar dakile cututtuka masu yaduwa NCDC da Ma’aikatar lafiya ta jahar kano sun sanar da samun karin mutune 14 masu dauke da cutar Coronavirus wato Covid-19 a Jihar Kano.
Wannan tasa adadin wadanda suka kamu da cutar a jihar Kano yanzu ya kama mutune 707 sannan kuma mutum 33 daga ciki sun rasu, sannan mutune 79 sun warke kuma an sallame su.