Gwamna Ganduje Ya Gana Da Dattawan Kano

 

Gwamna Ganduje Ya Gana Da Dattawan Kano

A soyayyar su da jihar su da ƙalubalen COVID-
19, dattawan jihar Kano waɗanda yawancin su ƙwararru ne, tsoffin ma’aikata, ƴan kasuwa da sauransu, sun gana da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta hanyar na’urar zamani wadda aka yi cikin bidiyo suna ganin juna tare da bada tabbacin bada gudunmawar su.
A ƙarƙashin shugabancin AB Mahmud SAN, dattawan sun bayyanawa gwamnan cewar, kulawar su shi ne yake nuna cewa sun shigo domin taya gwamnatin yaƙar cutar a fadin jihar.
Gwamna ya bayyana hakan ne lokacin da yake bayyanawa kafafen yaɗa labarai kan kwamitin karta kwana na jihar a Africa House dake gidan gwamnatin jihar Kano. 
Ya ƙara da cewar wasu hanyoyin da dattawan Kanon za su bayar da gudunmawar shi ne ta hanyar fasaha domin samar da ci gaba da ƙwarewa da sauran su, Ya kuma bayyana cewa suna da kulawa ta musamman a batun Almajiri da kuma kayan taimako na COVID-19 za mu yi aiki babu ƙaƙƙautawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.