GWAMNA TAMBUWAL YA KADDAMARDA BAYARDA TALLAFI GA YAN GUDUN HIJIRA

GWAMNA TAMBUWAL YA KADDAMARDA BAYARDA TALLAFI GA YAN GUDUN HIJIRA

 Yau Assabar ne Mai girma Gwamnan jahar Sokoto, Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal, CFR (Mutawallen Sokoto) ya kaddamarda bayarda tallafi ga yan gudun hijira ta hannun hukumar bayarda tallafin gaggawa ta jaha (SEMA) a garin Gandi dake cikin karamar hukumar mulkin Rabah.
Tun farko Mai ba Gwamna shawara na agajin gaggawa da Babban daraktan hukumar bayarda tallafin gaugawa ta jaha, Hon. Zubairu Magaji Albadau da Nasiru Alhaji Aliyu Sokoto sun bayyana irin kulawa da kuma damuwar Gwamnatin jahar Sokoto ga mabukata musamman yan gudun hijira. 
Sun kara da cewa Gwamnati na iya kokarinta domin ganin an saukakama bayin Allah mabukata musamman cikin wannan watan mai albarka da kuma lokacin bukukuwan sallah.
 Sannan daga karshe an wayar da kan al’umma akan cutar sarkewar numfashi watau corona virus.
Gwamna Tambuwal wanda yasamu wakilcin Maigirma Sakataren Gwamnatin jahar Sokoto, Mallam Saidu Umar FCNA (Mallam Ubandoman Sokoto) ya bayyana cewa wannan ba shine karo na farko ba da aka fara bayarda wannan tallafin, inda kuma ya basu tabbacin kulawa daga Gwamnati. 

Ya kara da cewa anayin dukkan shirye shirye  domin aga cewa dukkansu sun koma ga muhallansu, ya kuma ce wannan shirin anyishi ne domin asaukaka musu.
Abubuwanda kowane daga cikin dubban yan gudun hijira zasu amfana dashi sun hada da; Buhun shinkafa, buhun gero, buhun masara, buhun alkama da kuma shadda yadi goma (maza) su kuma Mata turmin atamfa kowane mutum guda sai kuma shanu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.