GWAMNATIN SOKOTO TA BAYAR DA TALLAFIN BUHUNHUNAN ABINCI GA MARAYU DA MAKAFI DA GURAGU HADI DA KURAME

GWAMNATIN JIHAR SOKOTO TA BAYAR DA TALLAFIN BUHUNHUNAN ABINCI GA MARAYU DA MAKAFI DA GURAGU HADI DA KURAME A KARAMAR HUKUMOMIN WURNO,RABAH, GORONYO,SABON BIRNI DA ISAH

Gwamnatin Jihar Sokoto Ta bayar Da Tallafin Buhunhuwan Abinci Ga Marayu Da Makafi Guragu Hadi Da Kurame Domin Samun Sassaucin Lalurorin Azumi Da Sallah.

Wannan yana Daya Daga Cikin Kudurin Mai Girma Gwamna Tambuwal domin ganin cewa An Kyautata Jindadi Da Walwalar Al’ummar Jihar Sokoto.
Za’a Ci Gaba Da Rarraba Kayan Tallafin Abincin Ne A Kowace Karamar Hukuma Dake Fadin Jihar Sokoto Karkashin Ma’aikatar Jindadi Da Walwala Ta Jihar Sokoto Wadda Hajiya Professor Aishatu Madawaki Isah Take Jagoranta.
Abubuwan Da Aka rarraba a kowace Karamar Hukuma Ashirin Da ukku (23) Sun Hada Da:
Buhunhuwan abinci 20, Mai Galan 20,
Atamfa 20,
Yadi 20

Leave a Reply

Your email address will not be published.