Kada a watsar da sauran marasa lafiya saboda kulawa da Masu Coronaviros

Gwamna ganduje ya yi kira ga ma’aikatan kiwon lafiya a jihar kano dasu daina watsi da wasu marasa lafiya Musamman wadan da ba cutar coronavirus ce ta kamasu ba.

 Ganduje ya yi Kiran ne alokacin da yake jawabi ya yin taron horar da shugabannin asibitocin jaha da Masu zaman kansu game, da rigakafin kamuwa da cutar Covid-19 da kula da ma’aikatan kiwon lafiya a asibitocin Jahar, wanda aka yi a hotel din Tahir Guest.
A cewar Ganduje, sanya ido ga sauran majinyata da ke fama da wasu cututtukan shi ma zai rage yawan mace-mace a jihar.
“Ya kamata a kula da mata da yara da Sauran Masu cututtukan da ya kamata a kula dasu; in ba haka ba, yaƙinmu da cutar covid-19 ba zai amfani ba, idan muka yi watsi da wasu cututtuka.
 Don haka, ina rokon ku daku mai da hankali ga marassa lafiyar mu domin ayyukan kiwon lafiyarmu, su kasance cikin tsabta ”in ji Ganduje.
Gwamnan ya kuma lura da cewa, samar da ingantaccen aiki abune mai kyau musamman a wannan lokaci, tare da nuna fatan cewa wannan horon da za’a bawa ma’aikatan kiwon lafiya na jihar don su kasance cikin shiri don dakile duk wata barkewar cutar a jihar.
Da yake jawabi a farko, mai gabatar da horon, Farfesa Bola Yinka, ya ce mahalarta taron 350, wadanda aka zabo likitoci ne daga ban garori daban daban wadan da suka hada da: likitoci, ma’aikatan jinya da masana kimiyya a duk asibitocin 42 na jihar, za a horar dasu kan kula da wasu cututtukan da kuma cututtuka masu yaduwa.
A cewarta, za a horar da mahalarta kan yadda za su kare kansu yayin da suke a fagen yaki da cututtuka masu kama da Coronavirus, tare da kara da cewa suma za su koma wuraren aikinsu tare da horar da sauran ma’aikatan. 

Leave a Reply

Your email address will not be published.