Kasar madagascar ta fice daga Kungiyar Lafiya ta duniya

Kasar madagascar ta fice daga Kungiyar Lafiya ta duniya WHO

Matashin jarumi Shugaban Kasar Madagascar Andry Rajoelina ya bayyana sanarwan ficewar Kasarsa daga cikin kungiyar hukumar kula da kiwon lafiya ta majalisar dinkin duniya (WHO), tare da yin kira ga sauran kasashen Afirka da su fice.
Dalilansa shine tun bayan da Kasarsa ta gano maganin cutar Coronavirus na gargajiya; manyan kasashen turai masu iko da WHO su ke ta yiwa maganin kafar-ungulu, har WHO ta fitar da sanarwan cewa kada ayi amfani da maganin gargajiya saboda makirci, kuma ganin cewa ba sune suka samu maganin cutar ba don su sayar su samu makudan kudade.
Shugaban ya kara da cewa akwai makirci da sharri da yawa a cikin sha’anin cutar Coronavirus wanda ke samun goyon baya daga hukumar kula da kiwon lafiya na majalisar dinkin duniya (WHO).
 Don haka daga yau Kasarsa Madagascar ta fice daga cikin WHO, sannan yayi kira ga sauran kasashen afirka da cewa suzo su karbi maganin Coronavirus kyauta.
Hakika wannan shugaba yana caccakar makircin yahudawa da nasara duk da dai sun fi kusa, amma inda ace wani shugaban Kasa ne Musulmi da sun masa sharri sun tayar masa da ‘yan tawaye an kawar dashi
Allah Ka karemu daga sharrin masu sharri, Ka yaye mana sharrin da makircin Coronavirus Amin

Leave a Reply

Your email address will not be published.