YAN JARIDA SUNE MASU RUWA DA TSAKI A HARKAR YAKI DA COVID-19 – GANDUJE

‘YAN JARIDA SUNE MASU RUWA DA TSAKI A HARKAR YAKI DA COVID-19 – GANDUJE
Idan ba tare da shigowar kokarin ‘yan jaridu ba, yakar COVID-19 ba zai samu ci gaba ba, in ji gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje.
Gwamnan ya bayyana kafafen yada labarai da sana’ar yada labarai a matsayin abune mai mahimmanci a yakin da ake yi da COVID-19 a Najeriya.
Ya sanar da hakan ne yayin da yake jawabi yayin taron kara wa juna sani na kwana daya kan Kare Kai daga kamuwa da cutar Coronaviros da kuma yadda ‘Yan Jarida zasu fadakar da al’umma.
 Taron wanda gwamnatin jihar Kano ta shirya tare da hadin gwiwar kwamitocin ministoci kan COVID-19 a Kano.
Ganduje yayi godiya ga gudummawar da ‘yan jaridu ke takawa a kokarinsu na tattara bayanai da kuma yada shi ga jama’a.
Ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za taci gaba da hada kai da kafofin watsa labarai a yakin da ake yi da cutar ta COVID-19 a jihar.
“Wannan taron yana da matukar muhimmanci. 
Mu’amala tsakanin Kungiyar Ministocin akan COVID-19 a Kano da kuma kafofin watsa labarai a cikin jihar na da matukar muhimmanci.
“Idan aka duba taken wannan bita, da farko dai, kare dan jarida da yan jaridu, Wannan yana faruwa ne saboda ‘yan Jarida sune masu aiki da kuma wayar wa Al’umma kai, kamar ma’aikatan lafiya.
“Kamar yadda ma’aikatan kiwon lafiya suka sadaukar da rayukan su, yan jaridu sun fi su shiga hatsari saboda suna da karancin masaniya game da cutar.
“Na yi imani cewa wannan bitar zai kara fadakarwa da kuma ilmantar da ‘yan jaridu game da hanyoyin bada kariya da kuma hanya mafi kyau don bayar da rahoton Corona Virus.
“Na yi matukar farin ciki da wannan bitar ta gudana a cikin Kano. 
Wakokilan kafofin watsa labarai suna da matukar muhimmanci a yakin da suke da cutar.
“Kafofin yada labarai suna yin aikin kwararru ne wajen isar da bayanan ga jama’a, sabo da ba tare da hakan ba mai yiwuwa ba za a yaba da kokarin ma’aikatan kiwon lafiya ba.
“Kafofin yada labarai sunyi matukar sanin al’adu da halayen mutane; kuma sun san hanya mafi kyau don sadar da bayanai ga jama’a kan hanyar da za su fahimta.
“Kafofin yada labarai sun san yadda jama’a suke ji kuma suna iya isar da sako iri guda – domin su iya yin abin da suke so tare da mika bukatun jama’a ga hukuma.
“Masu watsa labarai suna da nauyin ziyartar cibiyoyin gwaji, da wuraren tattara samfurori don ganin abin dake faruwa a wurin sannan su ba da rahoto iri ɗaya domin hukumomin su lura kuma suyi abin daya dace.”
Shi ma da yake jawabi a wurin bitar, Abdulsalam Nasidi, wanda ya wakilci Ministan Lafiya, Ehanire Osagie, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya yaba wa Ganduje da yazo da himmar horar da ‘yan jaridu dan kiyaye lafiya yayin gabatar da rahoton COVID-19.
“Ministan Kiwon Lafiya ya ambaci wannan taron ga Kwamitin Shugaban kasa kan COVID-19. Y
Ya yi hakan ne yayin wani taro ranar (Juma’a) lokacin da Shugaba Buhari yake wurin taron.
“Shugaba Buhari ya nuna godiyarsa ga gwamna Ganduje saboda baiwa kungiyar ministocin damar shirya wannan taron horar da ‘yan jarida.”
Kwamishinan yada labarai na jihar, Muhammad Garba, a cikin jawabinsa ya ce manufar shirin ita ce, “duba yadda za mu iya inganta hadin gwiwa tsakanin kafofin watsa labarai da kuma likitocin lafiya”.
Garba ya bayyana shirin da cewa, “yana da matukar muhimman ci kuma an samu nasara sosai,” ya kara da cewa ya tabo batun tsaro, da jindadin ‘yan jarida yayin bayar da rahoto akan COVID-19.
Daga cikin wadanda suka gabatar da jawabai a wurin taron har da Dr. Sani Gwarzo wanda ya yi magana a kan COVID-19 da Hadin Kai, Dr. Ovuoraye John ya yi magana game da kiyaye rayuka da kuma cutar COVID-19, Dokta Iroanya ya yi magana a kan mece ce COVID-19, yayin da Barr. Marta Okonofua ta yi magana game da Kamuwa da cuta, Yin rigakafi, da kuma kariya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.