Ganduje ya sauya ranakun fita zuwa lahadi laraba da juma’a

Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar ganduje ya canja ranakun sassaucin fita zuwa kwana uku lahadi laraba da juma’a inda za’a rinka fita daga karfe 10:00am na safe zuwa 2:00pm na Rana, awannin 12 a sati.
 
Sannan ranar sallah za’a fita karfe 6:00am na safe zuwa 2:00pm Sannan ba bukukuwan sallah akowace masarauta.
Haka Kuma ganduje ya amince da shawarwarin wakilan malamai su 30 na jihar Kano daga bangare daban daban akan bada izinin yin Sallar Jumaah da kuma sallar Idi. 
Gwamna ganduje ya bada wannan umarjin bayan tattaunawa mai tsawo da yayi dashi da Mataimakin sa da sauran jami’an Gwamnati tare da wakilam Malaman su 30 a dakin taro na Africa House a yanmacin ranar litinin.

 

Saboda haka za’a ci gaba da dage dokar hana zirga zirga, inda yanzu aka maida shi a ranakun lahadi da Laraba, da juma’a, sannan kuma yanzu Gwamnati ta kara da bada izinin sallar Juma’ah, sai kuma salllar Idi wadda ita ma aka yadda ayi ta amma banda shagulgulan Sallah.

 
Sannan an umarci Malaman Masallatan Jumaah da su tabbatar duk wanda zai shiga masallaci sai ya saka safar fuska wato face mask da kuma wanke hannu da saka sanitizers, sannan a tabbatar an raba sahu kuma an rage huduba tare da rage cinkoso.

Gwamnatin jiha ta kuma kafa Kwamaiti da zai lura da raba kayan tsaftace muhalli da safar fuska da sauran su ga masallatan jumaah na jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published.