GWAMNA BADARU YA UMARCI A BIYA ALBASHIN WATAN DA MUKE CIKI

GWAMNA BADARU YA UMARCI A BIYA ALBASHIN WATAN DA MUKE CIKI

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya bada umarnin ga hukumar kula da albashi da kudaden fansho da su biya albashin watan mayu da ga yau domin ma’aikata su sami damar shirin sallah.
Gwamnan, ya hori ma’aikatan da suyi kokarin samar da tazara tsakanin su musamma lokacin da suke kokarin gudanar da harkoki a cikin banki domin  dakile yaduwar annobar Coronaviros a jihar.
Alhaji Badaru Abubakar ya kuma yi kira da daukacin mutanen jihar jigawa da su kasance masu addu’a domin Allah yayi  mana maganin cutar da ta addabi duniya musamman a kwanaki goma na Ramadan.

Leave a Reply

Your email address will not be published.