MANYAN MAYAKAN BOKO HARAM 20 SUN BAKUNCI LAHIRA A BORNO

MANYAN MAYAKAN BOKO HARAM 20 SUN BAKUNCI LAHIRA A BORNO

Dakarun sojin Nigeria na rundinar OPERATION LAFIYA DOLE bataliya ta 130 sun samu nasaran hallaka manyan kwamandojin yakin Boko Haram/ISWAP guda 20 a yammacin jiya Lahadi a garin Baga jihar Borno
Tawagar ‘yan ta’addan suna tafe ne dauke da manyan makaman yaki da bama-bamai sun tunkari wani kauye a karamar hukumar Baga zasu tashi kauyen, sai dakarun sojin Nigeria suka musu kofar-rago suka hallakasu.
An kwato bindigogi kirar AK47 guda 6, harsashin bindiga guda 520 sai bama-bamai guda 36, 
 Sojojin Nigeria mutune 9 sun samu rauni a lokacin fafatawar, an kaisu asibitin sector 3 na sojoji ana musu magani, amma babu asarar rai daga bangaren sojojin.
A dayan bangaren, Boko Haram sun fitar da hotunan wasu manyan kwamandojin yakinsu da suka tabbatar da sojojin Nigeria sun hallakasu.
Ayanzu nasara tana samuwa a Arewa maso gabas, Boko Haram suna fuskantar mummunan turjiya daga rundinar sojin Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published.