El Rufa’i yaa ce Babu wanda zai shigo Kaduna daga Kano

Babu wanda zai shigo Kaduna daga Kano – El-Rufa’i

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Elrufa’i ya ce zai tabbatar babu mutumin da zai shiga Kaduna ranar Sallah kasancewar gwamnatin jihar Kano ta amince da gudanar da sallar Idi da Juma’a.
Yayin wani jawabi ga ‘yan jihar tasa da yammacin yau Talata, Gwamna Elrufa’i ya ce “ni da kaina zan je hanyar shigo wa Kaduna daga Kano na ga mutumin da zai shigo mana. 
Ya kara da cewa Cuta ta riga ta yi katutu a tsakanin mutane mu kuma mu bari su shigo mana da ita. Ba zai yiwu ba.”
Har wa yau, gwamnan ya zargi jami’an tsaro da ‘cin amana’ inda ya ce jami’an tsaro na karbar na goro domin barin jama’a su shiga Kaduna.
Sabanin wasu jihohi, Gwamna Elrufa’i ya ce kowa yayi sallar idi da Juma’a a gida domin hana bazuwar cutar korona dake yi wa duniya barazana.
Gwamna Elrufa’i dai bai fadi lokacin da ake sa ran bude jihar ba, inda mataimakiyarsa tace har yanzu basu gamsu da yanayin da cutar take a jihar ba, ballantana su bude jihar.
Daga karshe Malam Nasir El-Rufa’i ya yi wa malamai Allah-ya-isa inda yace “ko a Makka ba za ayi sallar Idi ba, amma mu a nan malamai sun hau munbari suna cewa mun hana sallah. Kuma sun sani. Saboda haka Allah ya isa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.