Ganduje ya kaddamar da gurin daukar sample na Masu cutar covid-19 a Bacirawa

Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya kaddamar da wajen daukar sample din mutanem da ake zargij suna da cutar Coronaviros wato Covid-19, wanda Gwamnatin jiha ta samar tare da hadin gwiwar E-Health Africa Clinics, wanda yake a asibitin Sheikh Waziri Gidado dake Bachirawa Kano. 

Wannan santa daya ce daga cikin santoci guda kusan 10 da ake daukar sample din domin yin gwaji a tabbatar ko mutum na dauke da cutar.
 Gwamna na tare da Mataimakin sa Dr Nasiru Yusuf Gawuna da Kwamishinan lafiya Dr Aminu Tsanyawa da sauran yan kwamitin kar ta kwana na Covid-19.

Leave a Reply

Your email address will not be published.