Ganduje ya kaddamar da wajen daukar sample na Masu covid-19 a Rano

Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya kaddamar da wajen daukar sample din wanda ake zargin suna da cutar Coronaviros wato Covid-19 na shiyyar Masarautar Rano wanda zai hada kananan hukumomin Rano, Bunkure da Tudun Wada. 

Sannan kuma Gwamnatin jiha ta samar da Motocin asibiti wato Ambulance da Pick Up, wadanda za’ai aiki dasu wajen daukar marasa lafiya masu dauke da cutar Corona wato Covid-19.
Gwamna Ganduje na tare da Mataimakin sa Dr Nasiru Yusuf Gawuna da Mai Martaba Sarkin Rano Alhaji Muhammad Inuwa Kabir da Kwamishinan lafiya Dr Aminu Tsanyawa da sauran yan kwamitin kar ta kwana na Covid-19.
   

Leave a Reply

Your email address will not be published.