Gwamna El Rufa’i zai gabatarwa mutanan kaduna jawabi Kai tsaye ta gidajen radiyo da kallo ta Facebook

Gwamna Kaduna Nasir El Rufa’i ya bayyana a shafin da na Facebook Mai suna {The governor of kaduna state} cewa zai gabatarwa mutanan kaduna jawabi Kai tsaye ta gidajen radiyo da talabijin da Facebook ga abinda gwamnan ya rubuta:

Ku kasance tare dani yau da misalin ƙarfe 2:00 na rana domin tattauna muhimman batutuwan game da matakan da muke ɗauka na yaƙi da cutar Kurona Bairos.

Kuna iya murɗa kowane tasha na rediyo dake Kaduna domin sauraren shirin.
 Haka kuma za ku iya kallo a shafukanku na Facebook.
Domin yin tambaya ko tsokaci, za a bayar da lambobin waya domin kira ko tura saƙon sms.

Leave a Reply

Your email address will not be published.