Shugaban Majalisar Limamain Kano, Sheik Falalu Dan Almajiri Ya Rasu

Shugaban Majalisar Limamain Kano, Sheik Falalu Dan Almajiri Ya Rasu

Khalifa Shaikh Falalu Dan Almajiri shugaban majalisar Limamai ta jihar Kano ya rasu a daren jiya Litinin.
Sheikh Falalu Dan Almajiri babban Malamin addinin Musulunci ne wanda duniyar Musulunci ta san da shi kuma Babban jigo ne a Darikar Tijjaniya na duniya baki daya.
Zuwa an jima kadan za a sanar da al’umma lokacin jana’izar sa a garin Kano.
Allah ya jikan sa da rahma, Allah ya gafarta masa ya bada hakurin wannan rashi. 
Ana da bangaren gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar ganduje ya Mike Sakon ta’aziya ga iyalai da majalisar limamai da tijjanawa da sauran jama’ar Kano bisa Wannan Babban Rashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.