Direba ya rasa ransa da motar sa sanadiyyar RAGEWA fasinja hanya

 Mallam Garba Direba ne Mai dauko Mota daga Cotonou Jamhuriyar Kasar Benin zuwa Nigeria.

Ya dauki passenger daga Gaya zuwa Dosso a Kasar Nijer, kafin suje Dosso lokacin shan ruwa yayi wato buda baki, sai passenger ya shawarce shi dasu karasa wani kauye anan kan hanyarsu zuwa Dosso don yin buda baki, anan dai passenger yace dashi nan kauyensu ne, ya shiga gida ya kawo musu abinci suka ci.
Bayan barinsu garin kafin su isa Dosso, Mallam Garba ya fara jin barci yana raba hanya, ashe wannan abinci da suka ci akwai guba aciki, a takaice passenger ya karbi mota ya kuma ajiye Mallam Garba a daji yana ta amai har Allah Ya karbi ransa, shi kuma yayi awun gaba da motar kiran highlander 2005 model.

Rayuwar duniya ta canza, zaka jawo mutum jikinka da niyyar ka taimakeshi, amma da zaran ya samu dama sai ya cutar da kai saboda cin amana, shiyasa yanzu idan zaka taimaki mutum, ka taimakeshi daga nesa, amma kar ka kuskura ka janwo wanda baka san tarihinsa ba jikinka, saboda Kaucewa irin Wannan.

Leave a Reply

Your email address will not be published.