El Rufa’i yayi watsi da bukatar malaman kaduna Kan sallar Idi

Gwamnan jihar kaduna Nasir El Rufa’i ya ce Tunda bamu bar Kirista sun yi bikin Ista ba, Musulmi su hakura da Sallar Idi.

“Anyi Sallar Ista da Good Friday Amma Duk shuwagannin Kirista babu wanda ya Fito yace abar kirista suje coci suyi cunkoso Sabo da sun san hadarin cunkuso wajen yada cutar nan sai shugabannnin Musulmi zasuce abar su suyi Edi.”
“Ciwon nan yana kana nan Hukumomi guda 9 a Jihar Kaduna Amma babu ko daya a Kudancin Kaduna Sabo da su can kudancin Kaduna suna bin doka sai bangaren da Musulmi suka yi yawa na arewacin Kaduna ne kawai ke hawa mashina suje makotan Jahohi Sallar Jumu’a ko suje Kano Kasuwanci daga nan su dawo da cutar, Amma su mutanen kudancin Kaduna basa karya doka.”
“Duk wanda bai yadda akwai Coronaviros ba, dan Allah yazo Government house gobe zan sa a kai shi inda marasa lafiyar suke, ya zauna dasu kwana biyu akwai masu tari akwai masu zazzabi bayan kwana biyu, inya ji a jikin sa sai mu tambaye shi”. Inji Gwamna Malam Nasir Elrufai.

Leave a Reply

Your email address will not be published.