Muhimman jawaban El Rufa’i da YAKAMATA kowa yasani

Gwamnan jihar kaduna Nasir El Rufa’i tare da mataimakiyarsa Dakta Hadiza Balarabe sun gabatar da muhimman jawabai Kai tsaye ta gidajen radiyo jiya talata da yakamata kowa yasani, ga jawaban kamar Haka

1.Babu ranar dage dokar hana fita.
2. Duk wanda yaje Kano ko wani gari Sallar idi to lallai karya dawo kaduna.
3. Maganar Almajiranci an rushe ta a jahar kaduna har abada.
3. kafin Sallah za’a rabawa al’umma kayan tallafi ga talakawa wanda kamfanin wayar hannu zasu gano.
4. Zuwa gobe zaa’a biya ma’aikata albashi don samun yin siyayyar shagalin Sallah.
5. Za’a kara yawan kasuwannin wucin gadi a jahar kaduna domin rage cinkoso da al’umma ke kuma akai.
6. Ba za’a bude masallatai ba saboda masu ihun cewa a bude basu fi Sudais ko saudia som addinin ba.
7. Mace macen da ake a Kano Corona ce ke kashe mutane, kuma an sani amma ba’ason fadi.
8. Makiya, jahilai, yan siyasa da muka kada zabe ne suke zuga mutane don su bata mu saboda kiyayyar mun kada su zabe, mun San haka shi yasa muka la’ance su.
9. Gwamna da kan shi zai tsaya hanyar Kano, Mataimakiyar Gwamna kuma zata tsaya hanyar Katsina, Sakataren Gwamnatin kuma hanyar Abuja a ranan Sallah domin hana masu shigowa da tsaraba shigowa.
10. Duk matakan da ake dauka ana dauka ne don kare al’umma.
11. Duk wanda yake shakkun cutar Corona to yaje gidan Gwamnati gobe za’a kai shi inda masu cutar suke don ya kwana biyu, in yaji a jikin shi sai ya bada labari.
12. An fasa saida Zaria Hotel, za’a maida wa Wanda aka sayarwa da kudin su domin asibiti Gwamnati zata gina.

Leave a Reply

Your email address will not be published.