Ganduje ya gana da Yan Majalisar Dattawa dana Tarayya na Jihar Kano

Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR a daren Jiya ya shirya ganawa ta Musamman da Yan Majalisar Dattawa dana Tarayya na Jihar Kano domin bayyana musu yanayin yadda Jihar take yaki da wannan cuta ta Coronavirus data addabi Jihar Kano, Najeriya dama Duniya baki daya domin su sheda kuma suga yadda Zasu Tallafawa Gwamnatin don yakar wannan cuta a Jihar Kano.

Yan Majalisar Tarayya sunzo a bisa Jagorancin Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Rt Hon Alhassan Ado Doguwa inda Yan Majalisar Dattawa aka samu Sanatan Kano ta Tsakiya Malam Ibrahim Shekarau.
Kwamishinan Yada Labarai, Malam Muhammad Garba na Kwamitin Tallafawa Mutane, ya yi bayanin yadda kwamiti tayi aikin rabon tallafi Kashi na farko da shirinsu na cigaba da Kashi na 2 
 Shima Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa da kuma Coordinata na Yaki da cutar Dr Tijjani Husain suka bayyana yadda harkokin gwaje gwaje da killace masu cutar yake gudana.
 Daga karshe Kwamishinan Ma’aikatar Ilimi Malam Sunusi Muhammad Kiru Shima yayi bayanin yadda aikin kwashe almajirai zuwa gidajen iyayensu yagudana a ciki da wajen Jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published.