Ganduje ya karbi ga garumar gudummawa daga KEDCO da kamfanin ZEDVANCE

Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya karbi kayan tallafi daga Kamfanin bada wutar lantarki mai kula da jihohin Kano, Katsina da Jigawa wato KEDCO, wanda suka kawo a yau kayan sun hada da buhun shinkafa mai nauyin 25KG guda 1,500

da kuma gallon din man girki mai lita 4 guda 1,500

da kuma safar fuska wato face mask.

Shugaban kamfanin Alhaji Tajuddeen Dantata da kuma Managing Director din kamfanin Alhaji Isiaku ne suka jagoranci mika kayan a fadar Gwamnatin jihar Kano.
Haka kuma kamfanin Zedvance shi ma ya kawo injin taimakawa numfashi wato ventilators guda 10, da safar fuska wato face mask guda 1,500, sannan kuma sun yi alkawarin gyara asibiti mai gado 100 domin a samar da wajen killace masu dauke da cutar Corona wato Covid-19 a Jihar Kano.
Gwamna Ganduje na tare da Mataimakin sa Dr Nasiru Yusuf Gawuna da shugaban jam’iyar APC na jiha Alhaji Abdullahi Abbas da kuma Kwamishinonin Lafiya dana yada labarai da shugaban Kwamitin tara tallafin Covid-19 na jihar Kano da sauran su.

Leave a Reply

Your email address will not be published.