Ganduje yayi alkawarin kawo karshen dukkan damuwar Kanawa

Ganduje yayi alkawarin kawo karshen dukkan damuwar Kanawa

A jiya Laraba ne gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya sanar da jama’ar jihar cewa yana yin duk abinda ya dace don dawo musu da kwanciyar hankalinsu.
Ganduje ya ce gwamnatinsa tana sane da matsalolin da jama’ar jihar ke ciki kuma yana kokarin shawo kan matsalolin.
Yace, daga cikin dalilin sassauta dokar takaita zirga-zirga a jihar da kara kwana daya na walwala shine don a bar mutane su cigaba da walwalarsu tare da kiyaye dokokin dakile yaduwar cutar.
“Gwamnati ta bada fifiko wajen kiyayewa tare da bada kariya ga rayukan jama’a. 
Hakan yasa ta takaita dokar hana zirga-zirga,” inji gwamnann.
A yayin jawabi ga limaman masallatan juma’a da limaman coci, gwamnan yayi kira garesu dasu fahimci annobar kuma su gane cewa dokokin da aka saka bana dindindin bane, na wucin-gadi ne don bada kariya ga rayuka.
“Akwai manyan matakan da aka dauka don dakile yaduwar cutar kuma ta wannan hanyoyin ne kadai za a iya tseratar da rayukan.
“Amma kuma mun bada ranakun bude harkokin jihar don bai wa jama’a damar neman kudi da yin ibada.
“Ranakun Laraba, Juma’a da Lahadi ne muka amince amma dole a kiyaye dokokin dakile yaduwar muguwar cutar da suka hada da saka takunkumin fuska, wanke hannu da kuma amfani da sinadarin tsaftace hannu,”.
A gefe guda, gwamnatin jihar Kano ta yi wa majami’u 31 na jihar feshin hana yaduwar cutar coronavirus.
Gwamnan ya sanar da hakan ne yayin taron da yayi da kungiyar mabiya addinin Kirista ta Najeriya (CAN) reshen jihar Kano a gidan gwamnatin jihar.
Kamar yadda yace, hadin kan mabiya addinin Kiristan da masu ruwa da tsaki ya zama dole wajen shawo kan annobar a jihar.
Gwamnan ya yi kira ga shugabannin da sauran mazauna jihar dasu kiyaye dokokin masana kiwon lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.