Gwamnatin jigawa ta fara biyan albashin wañnan watan na mayu

Ma’aikatan jihar Jigawa sun fara karbar albashinsu na wannan watan na mayu kamar yadda gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya bada umarni

Rahotanni na cewar tuni ma’aikata suka cika bankuna domin karbar albashin su domin gudanar da bukukuwan salla karama.
Ma’aikata da dama da aka tattauna dasu sun yabawa gwamna Badaru Abubakar bisa bada umarnin biyan albashi kafin lokacin biyan albashin bisa la’akari da halin da ake ciki na corona virus da kuma gabatowar bikin salla karama.
Ita ma a nata bangaren kungiyar kwadago ta jiha ta jinjinawa Gwamna tare da fatan ma’aikata zasu saka da wannan karamci wajen yiwa gwamnati addu’o’in bunkasa tattalin arziki da kuma samun sauki akan cutar coronavirus.
Idan za a iya tunawa a ranar litinin data gabata ne Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya umarci kwamishinan kudi na jiha Alhaji Babangida Umar Gantsa ya fara biyan ma’aikata albashi domin samun dammar gudanar da bukukuwan salla karama

Leave a Reply

Your email address will not be published.