Babu makawa sai tattalin arzikin Najeriya ya tabarbare – Ministar kudi

Babu makawa sai tattalin arzikin Najeriya ya tabarbare – Ministar kudi

Hasashe da bincike na tsimi da tanadi da hukumar kiddiga ta Najeriya ta gudanar ya nuna tattalin arzikin Najeriya zai shiga halin tabarbarewa da kashi -4.4 saboda annobar Coronavirus.
Premium Times ta ruwaito ministar kudi, Zainab Ahmad ta bayyana haka ga manema labarai bayan kammala taron majalisar tattalin arzikin kasa daya gudana a ranar Alhamis.
Hukumar kididdig ta gudanar da bincike, kuma sakamakon binciken ya nuna tattalin arzikin Najeriya zai shiga mawuyacin hali, da zai fadi da kashi -4.4,
“Amma duba da aikin da kwamitin tayar da komadar tattalin arzikin kasa take yi, muna sa ran zamu rage radadin faduwar tattalin arzikin.
“Idan muka dabbaka duk shawarwarin da aka bayar, faduwar tattalin arzikin zai ragu da kashi -0.4, duk dai yadda aka yi sai mun fuskanci tabarbarewar tattalin arziki.
Kokarin da muke yi shi ne mu tabbata faduwar batayi zurfi ba, ta yadda da zarar an shiga 2021 zamu farfado.” Inji ta.
Najeriya na cikin kasashen da suka fi fuskantar matsala sakamakon annobar Coronaviros, saboda babbar hanyar samun kudinta shi ne sayar da man fetir, wanda a yanzu darajarsa ta karye warwas.
Karyewar darajar man na nufin kudin shigar kasar sun ragu kenan, haka zalika ga shi kasar ta dakatar da duk wasu harkokin kasuwanci saboda gudun yaduwar annobar cutar Coronaviros.
Hakan ya sa dole Najeriya ta sake bude kasuwanci duk da cigaba da ruruwar cutar Coronavirus a kasar, kamar yadda minista Zainab tayi bayani.
“Muna cikin mawuyacin hali, kalubalen da muke fuskanta guda biyu ne, akwai matsalar kiwon lafiya, akwai kuma matsalar tattalin arziki, koda muke kokarin shawo kan matsalar kiwon lafiya, dole kuma mu lura da yadda zamu tallafa ma tattalin arzikin kasar don gudu rugujewar ta.
“Dole mu ciyar da jama’a, amma babu yadda za’a ciyar da jama’a ba tare da an yi noma a gona ba, muna da yawan jama’a don haka bamu son shiga hatsari, kuma bamu da isashshen abinci da zai rage radadin matsalar.” Inji ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published.