Dokar hana fita na nan daram a Kaduna, babu gudu babu ja da baya

Dokar hana fita na nan daram a Kaduna, babu gudu babu ja da baya – Gwamnati kaduna

Gwamnatin jahar Kaduna ta tabbatar da dokar hana fita a jahar Kaduna, sa’annan ta dauki alwashin tabbatar da dokar hatta a ranar karamar Sallah ta bana.
Gwamnatin ta sanar da haka ne bayan taron majalisar tsaro daya gudanar a ranar Alhamis a fadar gwamnatin jahar, inda ta bayyana Laraba da Alhamis a matsayin ranakun fita kawai.
Kwamishinan tsaro na jahar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar, inda yace an baiwa hukumomin tsaro daman dabbaka dokar a sauran ranaku.
Don haka ake kira ga jama’a su bi dokokin da aka tsara, da suka hada da hana tafiye tafiye, hana duk wani taron ibada da kuma hana tarukan biki, ko na siyasa ko kuma na wani hidima.
Gwamnatin ta ce dalilinta na daukan wannan mataki shi ne don kare rayukan al’umma, don haka ake rokon jama’a suyi hakuri da halin da ake ciki domin kare kansu da kowa da kowa.
Kwamishinan ya kara da cewa a kokarinmu na tabbatar da bin doka da oda, jami’an tsaro za su kara kaimi wajen gudanar da sintiri, haka zalika za’a karfafa matakan tsaro game da hana shige da fice a jahar tun daga bakin iyakar jahar.
“Jami’an tsaro za su kasance masu nuna ya kamata da kwarewa wajen aikinsu, ana iya sanar da mu duk wani cin zarafi na jami’an tsaro a lan lambobin 09034000060 da 08170189999.” Inji sh

Leave a Reply

Your email address will not be published.