Duk ma’aikacin lafiyar da yaki zuwa aiki ya Kori kansa daga aiki – El-Rufai

Duk ma’aikacin lafiyar da yaki zuwa aiki ya  Kori kansa daga aiki  – El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya gargadi ma’aikatan asibitocin jihar, daya hada da nas-nas da likitoci cewa duk wanda ya biye wa kungiyar likitoci reshen jihar yaki zuwa aiki, ya dauka tamkar ya yi sallama da aikin ne Kwata-kwata.
A takarda da gwamnatin jihar ta fitar ranar Alhamis wanda Muyiwa Adekeye ya sakawa hannu gwamna Nasir El-Rufai ya ce gwamnati tana dukkan abinda ya Dace domin kula da ma’aikatanta.
”Ya ce Kira da a fara yajin aiki a wannan yanayi na Korona, goga wa gwamnati kashin kaji kawai amma Babu dalilin yin haka.
” Duk ma’aikacin da yake son ya ci gaba da aiki da gwamnatin Kaduna yaje Inda yake aiki ya saka hannu a rajista.
” Wadanda kuma ba su son yin aikin kada su kuskura suce za su datse kofofin asibitoci, ko wuraren kiwon lafiya, Ko kuma suce za su muzantawa wadanda suka zo aiki. Yin haka karya doka ne.
” Ba ma’aikatan lafiya bane kawai za’a zaftare musu Kashi 25 bisa 100 na albashin su, su ma ma’aikatan gwamnati ne, Kuma su ba shafaffu da Mai bane da za a cire wa kowa amma a ki taba nasu albashin.
Gwamnati ta ce wannan Kashi 25 bisa 100 data zaftare a albashin ma’aikatan jihar kamar sadaka ne suka yi don tallafa wa talakawa da fakiran Kaduna da albinci a wannan lokaci da ake zaman gida dirshan da babu ranar fita.
Bayan haka kuma, gwamnatin Kaduna ta ce ay su ma’aikatan lafiya ma ana biyan alawus alawus a duk rana da wasu ma’aikatan basu samu ba. Wasu naira 5000, wasu 10,000, wasu kuma 15,000.
PTH

Leave a Reply

Your email address will not be published.