Buhari ya haramta wa ministoci hukunta shugabannin cibiyoyi da ke karkashinsu

Buhari ya haramta wa ministoci hukunta shugabannin cibiyoyi da ke karkashinsu

Gwamnatin shugaba Buhari ta haramta wa ministocinta sallamar shugabannin cibiyoyin dake karkashin su kai tsaye.
A halin yanzu, sabon tsarin ya kara karfafa ikon ofishin sakataren gwamnatin tarayya ta fuskar ladabtarwa, kamar yadda wata takarda da Premium Times ta samu.
Takardar mai kwanan wata 19 Mayu wacce kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya aminta da ita, ya nuna tsananin damuwarsa a kan yadda ministoci ke tsige shugabannin wasu cibiyoyi dake karkashin su da kuma illar hakan ga daidaituwar cibiyoyin.
An tura takardar ga kowanne ministan da kuma sauran manyan jami’an gwamnatin wadanda suka hada da shugabar ma’aikatar tarayya, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, shugabannin tsaro, gwamnan babban bankin Najeriya da kuma manyan sakatarorin gwamnati.
A baya, ministoci na da karfin ikon ladabtar da shugabannin kungiyoyi, hukumomi ko sashen da suke kula dasu. 
Ladabtarwar na kamawa daga dakatarwa da kuma kora kwata-kwata.
A misali, a watan Janairu, ministan wutar lantarki, Sale Mamman ya tsige Damilola Ogunbiyi da Marilyn Amobi a matsayin shugabannin cibiyar wutar karkara ba tare da sanin fadar shugaban kasa ba, ko kuma gurfanar dasu a gaban kwamitin ladabtarwa.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya so dawo dasu kan aikinsu amma kuma sai ministan ya sake korar manajan daraktan kamfanin rarrabe wutar lantarki na Najeriya, Usman Mohammed, tare da wasu daraktoci hudu, duk da yace ya nemi izinin shugaba Buhari.
Wannan takardar da sakataren gwamnatin tarayyar ya fitar na bada kariya ga shugabannin cibiyoyi daga ministocin dake kula dasu, don hakan ne kadai zai dakatar ko hana sallamarsu a yayin da wani abu ya taso.
Haka zalika, barazanar ministoci na kora, matukar aka kama shugaban cibiya da rashin daukar aikinsa da muhimmanci, bazai yi aiki ba yanzu ba.
Kamar yadda takardar ta bayyana, idan shugaban cibiya yayi laifi, ana bukatar ya mika koken ta hannun babban sakatarensa zuwa majalisar zartarwar cibiyar don fuskantar hukuncin daya dace.
Daga nan ne majalisar zartarwar za ta iya mika wasikar tuhuma ko kuma ta shawarci ministan a kan abinda ya dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published.