Dakarun sojin saman Najeriya sun ragargaza ‘yan ta’adda 135 a Katsina da Zamfara

Dakarun sojin saman Najeriya sun ragargaza ‘yan ta’adda 135 a Katsina da Zamfara

Rundunar sojin Operation Hadarin Daji ta tarwatsa sansanin ‘yan bindiga tare da nasarar halaka a kalla 135 daga cikinsu.
Dakarun sojin saman sun kai samamen ne tsakanin ranar 22 zuwa 23 na watan Mayun 2020 a wurare da dama na maboyar ‘yan bindigar da ke jihohin Katsina da Zamfara.
Daga cikin sabon salon kakkabe ‘yan bindigar da suka gallabi jama’ar jihohin Katsina da Zamfara, gwamnatin tarayya ta kara tura dakarunta yankin.
A makon daya gabata ne ‘yan bindigar suka saka yankunan a gaba inda suke yi wa jama’a kisan kiyashi tare da kwashe musu Shanunsu.
Bayan kiran da shugabannin yankin tare da masu fada aji suka dinga yi wa gwamnatin tarayya, an tura karin sojoji daza su kawo karshen lamarin.
Hakazalika, sojin saman sun kai hari a sansanin Hassan Tagwaye da na Alhaji Auta tare da na Maikomi.
Shugaban dakarun sojin saman Najeriya ya jinjinawa rundunar Operation Hadarin Dajin a kan wannan gagarumar nasarar
Ya umarcesu dasu dage wajen tabbatar da cimma manufar shugaban sojin Najeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai, na kakkabe ‘yan bindigar tare da dawowar zaman lafiya yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.