SAKON SHEKH DAHIRU BAUCHI GA AL’UMMA BAYAN GUDANAR DA SALLAR IDI A GARIN BAUCHI

SAKON SHEKH DAHIRU BAUCHI GA AL’UMMA BAYAN GUDANAR DA SALLAR IDI A GARIN BAUCHI

Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bayyana cewa shi lamarin Ganin wata Aminci ake Bukata kuma Alhamdulillah mun samu Aminci da tabbaci kan haka Daga Amintattun mu Domin haka muka Gabatar da Sallah IDI a yau.


Fahimtar mu da Addini babu tsanani ko Zargi a cikin sa hujja kawai ake nema in ka Gamsu ka samu yakini kan Ganin watan Ramadan kayi Azumi in anga watan Shawwal bisa Hujjoji da Sharadi kasha ruwa, wanda Suka Amince da kai suma su sha, kaine madogaran su sun Amince cewa baza ka musu Karya ba.


wannan yakinin kawai ake nema ko a Lahira.


Shehin Yakara da cewa A zamanin Annabi (S A W) Mutane basu ga wata ba, sai Annabi S. A.W yace a cika Azumi 30, ranar da ake Azumin da Rana wani mutumi yazo ya bayyana wa Annabi cewa yaga Jinjirin wata Jiya, nan take Annabi yace kowa ya karya azumin sa, toh ballanta wanda Mutanen da Muka yarda dasu adadi masu yawa duk sun gani.


Muna fatan Allah ya karbi ibadun mu ya kuma Maimaita mana yasa Munyi Azumi a Sa’a Cikin yardan sa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.