Sarkin Yawuri A Jihar Kebbi Ya Umarci Al’umarsa Su Ajiye Azumin Yau Asabar.


Mai martaba Sarkin yawuri Dakta Muhammad Zayyanu CON ya ce bisa matsololin da aka Samu na tattara bayanai dangane da Ganin watan sallah ajiya, ansami ganin watan sallah agarin yawuri da ke wayanta.

 Don Haka Mai martaba Sarkin yawuri ke Kara tunatar da dukkanin al'ummar musulmi cewa Wadanda suka tashi da azumi ayau agarin yawuri su ajiye saboda matsalolin da aka samu.

Haka Kuma baza asami damar yin sallar idi ayau ba, agarin yawuri saboda kurewar lokaci, Amma gobe idan Allah yakaimu da misalin karfe 9:00am za'a fito sallar idi a masallatai guda goma na juma'a da aka ware.
 
Masallatan sune masallacin juma'a na garkan sarki da masallacin juma'a na gudun gada da masallacin juma'a na unguwar wali da masallacin unguwar malamai da masallacin juma'a na Alh Usman so dangi da masallacin umaru Kani da masallacin juma'a guda biyu na yarabawa Suma za'ayi sallar idi anan da Kuma masallacin yamo.

Leave a Reply

Your email address will not be published.