Ba zamu Cigaba da Tsawaita Rufe Mutane Ba~ Shugaba Buhari


Ba zamu Cigaba da Tsawaita Rufe Mutane Ba~ Shugaba Buhari.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shaidawa ‘yan kasar cewa, matakan killace su da kuma takaita zirga-zirga da suka gurgunta lamurran yau da kullum saboda annobar coronavirus, baza su cigaba da wanzuwa na lokaci mai tsawo a nan gaba ba.
Shugaban ya ce gwamnati na bibiyar halin da ake ciki kan matakan yaki da cutar, kuma za a cigaba da sassautawa, da ma janye matakan idan lokaci yayi.
Cikin sakon taya murnar zagayowar Sallah karama daya aikewa ‘yan Najeriya ta hannun kakakinsa malam Garba Shehu, Buhari ya taya jama’a alhinin yadda annobar coronavirus ta yi tasiri wajen sauya yanayin Ibada, zamantakewa da kuma durkusar da tattalin arzikin kasar.
Sai dai shugaban ya bukaci ‘yan Najeriya dasu cigaba da nuna juriya gami da fata mai kyau, da kuma bin dokokin gwamnati da sharuddan kwararru a fannin lafiya, domin gaggauta ganin bayan annobar ta coronavirus.

Leave a Reply

Your email address will not be published.