BOKO HARAM/ISWAP SUN KWASHI KASHINSU A TAFIN HANNU

BOKO HARAM/ISWAP SUN KWASHI KASHINSU A TAFIN HANNU

Mayakan sojojin kundunbala na gwamnatin tarayyar Nigeria suna cigaba da mamayar maboyar ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP a yankin tafkin Chadi.
Daga ranar 11-5-2020 zuwa jiya juma’a 22-5-2020 sojojin Nigeria sun samu nasara mai yawa a yakin da suke da wadannan ‘yan Boko Haram.
A kalla sojoji sun hallaka manyan kwamandojin yakin Boko Haram guda 35, ga jimillan adadin makaman yaki da aka kwato daga hannun ‘yan ta’addan.

1. 4 x BHTs Gun trucks
2. 13 AK 47 rifles
3. 1 x Anti Aircraft Gun
4. 139 x Rounds of 7.62 mm Special Ammunition
5. 250 x rounds of 12.7 mm AA Ammunitions
6. 11 x magazines
7. 4 x 36 hand grenades
8. 1 x LG3 Bomb
9. 2 x Cartridges
10. 2 x motorcycles
11. 23 x bicycles
12. 1x dane gun
13. 2 x pushcarts
14. 3x BHTs Flags
15. 1 x BHTs’ uniform
16. 1x lister grinding machine
17. 1 x 2GB memory card
18. 1 x flash drive
19. 2 x techno cell phones
20. 10 x litres of PMS
21. 1 x solar panel charger
22. Clothings and assorted food items.
Shugaban sojojin Nigeria ya yabawa nasaran da sojojinsa ke samu tare da agajin ‘yan kato da gora da ‘yan banga da mafarauta, kuma ya umarci dakarunsa dasu kara kokari da himma wajen kawo karshen ta’addancin Boko Haram daga doron duniya nan da kankanin lokaci
Muna rokon Allah Ya taimaki sojojin Nigeria Ya tabbatar musu da cikakken nasara a kan ‘yan Boko Haram da masu tallafa musu ta kowace hanya Amin

Leave a Reply

Your email address will not be published.