Ku Hukunta Duk Wanda Ya Karya Doka- El Rufa’i Ga Jami’an Tsaro

Ku Hukunta Duk Wanda Ya Karya Doka- El Rufa’i Ga Jami’an Tsaro

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna,
Alhaji Umaru Muri ya yi kira ga mutane su bi dokokin da aka kafa domin kare kai daga cutar Coronavirus data zama annoba a fadin Duniya.
CP Umaru Muri ya bayyana cewa za suyi maganin duk wanda ya saba dokar zaman gida da shiga cinkoso a jihar Kaduna a yayin da musulman Duniya ke yin bikin karamar sallah.
Umaru Muri ya fitar da jawabi ta bakin jami’in dake magana da yawun ‘yan sandan Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya na mai cewa za suga bayan duk wani ko kungiyar data saba doka.
“Rundunar ‘yan sanda na reshen jihar Kaduna suna sanar da mutane cewa ta tsara yadda za tabi wajen ganin an bi dokar zaman-gidan da gwamnatin jiha tasa domin yaki da annobar COVID-19 da kuma zuba dakaru domin maganin ta’adin migayu a lokacin bikin sallah a fadin jihar.”
Jawabin Jalige ya kara da cewa: “A game da haka, rundunar ta baza jami’an ta-kife da masu fararen kaya su tsare ko ina, su kuma rika sa ido a wuraren da za a iya yin barna domin su tabbatar cewa an bi dokar zaman-gidan da aka kafa, sannan a samar da tsaro a cikin jihar”.
A karshen kwamishinan ‘yan sandan ya ce: “Rundunar ta na kara tabbatarwa mutanen jihar Kaduna cewa a shirya take ta saurari wani koke na ganin bayan duk wani mutumi ko kungiya dake kokarin sabawa takunkumi da dokar hana shiga cinkoso a lokacin da ke wannan biki.”

Leave a Reply

Your email address will not be published.