Yadda Buhari yayi sallar idi a gida da iyalansa
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya gudanar da Sallar Eidin sa a farfajiyar fadar shugaban kasa daga shi sai iyalin sa.
Tun farko dai shugaba Buhari ya bayyana cewa zai yi Sallar sa ne a gida tare da iyalin sa domin gujewa cunkoso tare da dakile yaduwar cutar Corona.