Buhari ya umarci Ibrahim Gambari ya soke ayyuka da nade-nade guda 150 da Abba Kyari yayi ba da izinin Buhari ba

Shugaba Buhari yasa sabon shugaban ma’aikatansa, Ibrahim Gambari ya soke abubuwan da Marigayi Abba Kyari yayi bada Umarninsa ba.

Rahotanni daga fadar shugaban kasa na cewa akwai rade-radin cewa shugaba Buhari ya sa sabon shugaban ma’aikatansa, Ibrahim Gambari ya soke duk wani abinda marigayi Abba kyari yayi bada Umarninsa ba.
Rahoton yace an gano wasu ayyuka da nade-nade har 150 da marigayi Abba Kyari yayi ba tare sa umarnin shugaban kasa ba kamar yadda, Guardian ta ruwaito.
Jaridar ta tuntubi me magana da yawun shugaba kasar, Femi Adesina akan wannan batu amma bai bata amsa ba.
Hakanan shima dayan me magana da yawun shugaban kasar, Garba Shehu bai bayar da amsa ba da aka mai tambaya kan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.