Ganduje ya biya tarar masu karamin laifi mutune 294A a gidan gyaran Hali na gwauran dutse

Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya kai ziyara gidan gyaran hali na Goron Dutse kuma ya biya tarar masu karamin laifi  mutune 300 kamar yadda ya saba bisa al’ada duk Sallah babba da karama.

 Wanda wannna yayi daidai da kiran shugaban kasa Muhammad Buhari na arage cunkoso a gidajen gyaran Hali na kasar nan musamman a wannan yanayi na annobar corona wato Covid-19.

Gwamna Ganduje na tare da Mataimakin sa Dr Nasiru Yusuf Gawuna da Sakataren Gwamnatin jiha Alhaji Usman Alhaji da shugaban jam’iyar APC na jiha Alhaji Abdullahi Abbas da sauran su.
A karshe gwamnan da shugaban gidan gyaran halin sun bukaci Wadanda aka yantar da sukasance Masu kyawawan halaye, kuma su guji sake aikata laifuka anan gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.