mutane 229 sun kamu, 48 sun warke, 7 sun rasu sanadiyyar cutar covid-19 a Najeriya

Sabbin mutane 229 sun kamu, 48 sun warke, ya yin da mutane 7 suka rasu sanadiyyar  cutar covid-19 a Najeriya.

Aranar litinin 25/5/20  cibiyar dakile cututtuka masu yaduwa NCDC ta tabbatar da Samun karin mutane 229 da suka kamu da cutar sarkewar numfashi ta covid-19 a Najeriya Wanda jimillar wadanda suka kamu da cutar yakai 8,068 yayin da mutane 2,311 suka warke, inda mutane 233 suka rasu.
Wadannan sune jihohi da adadin mutanen da suka kamu da cutar covid-19 Aranar litinin a Najeriya
 Lagos-90 
Katsina-27 
Imo-26 
Kano-23 
FCT-14 
Plateau-12 
Ogun-9 
Delta-7 
Borno-5 
Rivers-5 
Oyo-4 
Gombe-3 
Osun-2 
Anambra-1 
Bayelsa-1 

Leave a Reply

Your email address will not be published.