Mutane 32 sun warke ya yin da aka bude garuruwan uku a jigawa

AN SALLAMI MUTNE 32 MASU DAUKE DA CUTAR COVID-19, AN KUMA DAGE DOKAR ZAMAN GIDA A GARURUWA UKU

Kwamitin yaki da cutar coronavirus na jihar Jigawa ya sallami mutane 32 sa’annan ya dage dokar zaman gida da aka sanya a garuruwan Birnin Kudu da Gwaram da kuma Gumel.
Haka kuma kwamitin ya sanya dokar kulle agarin Kaugama sakamakon bullar cutar coronavirus a yankin.
Shugaban kwamitin kuma kwamishinan lafiya Dr Abba Zakari Umar be ya sanar da hakan ga manema labarai a cibiyar killace almajirai dake sansanin horas da masu yiwa kasa hidima dake Fanisau Dutse.
Yace an dage dokar zaman gida da aka sanya a garuruwan uku ne sakamakon kammala gwajin wadanda suka yi da mu’amula da masu cutar a wadannan wurare.
Dr Abba Zakari ya kara da cewar za a kulle garin kaugama ne sakamakon samun cutar, da nufin tantance wadanda suka yi mu’amula da masu cutar domin yi musu gwaji.
A yanzu yawan wadanda suka warke kuma aka sallama sun tasamma 143.
Kwamishinan ya kara da cewar a yanzu haka mutane hamsin 50 suka rage masu dauke da cutar da aka killace a cibiyoyi uku da ake dasu a birnin jiha Dutse.
Daga nan kwamishinan yayi fatan garuruwan da aka bude zasu kiyaye da shawarwarin ma’aikatan lafiya wajen gudun yaduwar cutar inda suma jama’a yayi fatan zasu kiyaye da dokokin wanke hannaye da sanya safar rufe hanci da baki da kuma bada tazara.

Leave a Reply

Your email address will not be published.