Sojoji sun kashe mahara 200 a Katsina da Zamfara


Sojoji sun  kashe mahara 200 a Katsina da Zamfara


Akalla Mahara 200 ne jiragen saman yakin Najeriya suka yi ragaraga dasu a dazukan Jibia dake jihar Katsina da Kurmi, a jihar Zamfara.

Ko odinaton yada Labaran sojin Najeriya, John Enenche ya ce an yi wa wani maboyar mahara daka Ibrahim Mai a Jibiya luguden wuta ta sama kuma sun kashe mahara da dama. 

Eneche ya ce Sojoji sun samu labarin cewa a wannan wuri ne ake jibge shanun da aka sace wa fulani kuma Nan ne maboyar gaggan masu garkuwa na maharan.

Bayan haka sojojin saman sun ragargaji Wasu maharan a Kurmi, karamar Hukumar Zurmi, a jihar Zamfara.

Babban Hafsan Sojojin Saman Najeriya ya nuna farin cikin sa matuka bisa wannan nasara da dakarun sa suka samu yana mai cewa za a tura wasu jiragen zuwa yankin Kaduna, Neja da Kogi domin fatattakar iren-iren wadannan bata gari.

Leave a Reply

Your email address will not be published.