YADDA SARKIN KANO AMINU ADO YAYI SALLAR IDIN FARKO TARE DA GANDUJE

YADDA SARKIN KANO AMINU ADO YAYI SALLAR IDIN FARKO TARE DA GANDUJE

Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya laharci Idin karamar Sallah tare da Mai Girma Mataimakin Gwamna Dr Nasiru Yusuf Gawuna da Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da shugaban jam’iyar APC Alhaji Abdullahi Abbas da Chief of Staff na Gwamna Hon Ali Haruna Makoda da tsohon Sakataren Gwamnatin jiha Alhaji Rabiu Sulaiman Bichi da sauran manyan jami’an Gwamnati da Hakimai da al’ummar musulmi wanda limamin Kano ya jagoranta a filin Idi dake kofar Mata.
Mai martaba Sarki da gwamnan da sauran manya sunyi sallar idin acikin gilas na masallacin, ta hanyar bada tazarada Sanya Safar rude Baki da hanci.
An rabawa  masallata da dama takumkumin rufe baki da hanci, Sannan an basu sinadarin kashe kwayoyin cuta ( hand snitizer ) sun shafa domin dakile yaduwar annobar cutar covid-19.

Leave a Reply

Your email address will not be published.