Ana saran za’a bude Makarantu a Najeriy a watan yuni

Ana saran za’a bude Makarantu a Najeriy ~ Gwamnatin Tarayya.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewar; dukkan makarantu, jami’o’i da Kwalejoji za su dawo domin cigaba da karatu a ranar 8 ga watan Yuni 2020.
Sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya, kuma shugaban kwamitin kula da cutar Covid-19 na kasa, Boss Mustapha ne ya tabbatar da hakan ga al’ummar Najeriya da kuma dalibai a yayin da yake zantawa da mambobin kwamitin kula da cutar Covid-19.
Boss Mustapha, ya ce, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bude dukkan makarantun gwamnati dana kudi da Bankuna, da kuma wuraren bauta bayan karshen wa’adin kulle na biyu wanda za’a kawo karshen sa a ranar 1 ga watan Yuni 2020. 
Daga nan kuma abubuwa su cigaba da wakana kamar yadda aka saba a ranar 8 ga watan Yuni 2020.

Leave a Reply

Your email address will not be published.