Za ayi dauri da cin tarar duk malamin daya dauko Almajirai a kaduna

Gwamnan Kaduna Nasir El Rufa’i ya ce Duk wani malamin daya dauko yara da sunanan Almajirci zai fuskanci fushin gwamnati, kuma za a daure shi kuma aci shi taran naira 100,000 zuwa 200,000 akan kowani yaro.


Ya kara da cewa duk almajiran da aka dawo dasu daga wasu jihohin kasar nan gwamnati za ta horas dasu ta yi musu wankan tsafta domin zama mutane kuma ta saka su a makarantu kusa da iyayen su.

Ya ce kowa zai yi karatun Islama da boko amma kuma wannan karon a kusa da iyayen sa. ” Sannan kuma da zaran an kammala girgije wadannan yara sun yi ta-tas za mu mika su ga iyayen su hannu da hannu, kuma mu saka su a makaranta ga su ga iyayen su.

Haka Kuma El Rufa’i ya gargadi iyaye dasu kasa kunnuwan su, su sauraren shi, cewa daga yanzu duk Wanda aka samu ya tura dansa almajirci zuwa wani wuri, zai iya fuskantar dauri da cin tara.

El-Rufai ya yi wannan gargadi ga iyaye ne a wajen horas da Almajiran da gwamnatin Kaduna ta killace tana musu wankan tsafta domin zama mutane a cikin al’umma a Kaduna.

El-Rufai ya ziyarci makaranta Kurmin Mashi inda aka killace almajirai ‘yan asalin jihar da aka dawo dasu daga jihar Nasarawa su 200.

 nata jawabin kwamishiniyar jin dadin al’umma Hafsat Baba, ta shaida cewa jihar Kaduna ta karbi almajirai akalla 900 daga jihohin Kano, Bauchi, Plateau da Nasarawa.

Sannan kuma gwamnati ta gode wa asusun UNICEF kan tallafa mata da yake yi wajen tufatar da yaran da samar musu da abin da suke nema.

Leave a Reply

Your email address will not be published.