Kano ta yiwa mutane 1,018 gwajin cutar covid-19 a sati daya

KANO TA GABATAR DA SAMFURA GUDA 1,018 DON GWAJIN CUTAR COVID-19 A CIKIN MAKO GUDA.

Kwamishinan yada labarai kana memba na Kwamitin bada tallafin cutar covid-19 na jihar Kano, Malam Muhammad Garba ya ce sun gabatar da samfurori 1,018 daga cikin wadanda ake zargi da cutar COVID-19 a cibiyoyin gwaji uku na jihar don gwajin cutar a tsakanin 23 zuwa 30 ga Mayu.
Kwamishinan, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ayau Lahadi ya ce bisa la’akari da bayanai da aka samu daga kungiyar Task Force a kan  cutar COVID-19, daga wannan adadi, an gano cewa 72 sun kamu.
Ya kuma kara da cewa a daidai wannan lokacin, 881 daga cikin samfuran da aka gwada ba su da cutar, yayin da 42 ke kan ci gaba da gwajin, 28 suna kan sake maimaita gwajin, wanda a cikin sharuddan da likitoci suka nuna, yana nufin dole ne a maimaita gwajin bayan gwajin farko wanda bai nuna akwai ko babu cutar ba.
Malam Garba yayi karin bayani cewa suna jiran bayanai na sakamako daga dakunan gwaje-gwaje a Kano.
  National Reference Laboratory, na Abuja  ya nuna cewa Jami’ar Bayero, Kano tana da mafi girman wajen gwaje-gwajen samfurin, biyo bayan asibitin koyarwa na Aminu Kano.
Kwamishinan, ya yin da yake sake jaddada kudirin gwamnati na yakar cutar, ya yi kira ga jama’a dasu lura da kiyaye lafiya da kiyaye ka’idodin likitoci da Masu ruwa da tsaki wadan da suka hada da nisantar jama’a, amfani da takunkumin fuska, wanke hannu da kuma tsabtace lafiyar jiki, da saran su.

Leave a Reply

Your email address will not be published.