Buhari ya sassauta dokar kulle a kano na tsawon sati hudu
Buhari ya sassauta dokar kulle a kano na tsawon mako hudu
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sassauta dokar kulle ta mako huɗu daya saka a Jihar Kano da zummar daƙile yaɗuwar cutar korona.
Kwamitin na shugaban ƙasa mai yaƙi da cutar korona a Najeriya ya ce za a buɗe dukkanin kasuwanni, yayin da wa’adin farko na mako biyu na sassauta dokar kulle ke cika aranar Litinin.
Sai dai Dr. Sani Aliyu, babban jami’i a kwamitin, ya ce za a buɗe su ne na tsawon mako huɗu sannan kuma gwamna ne zai tsara yadda za a buɗe kasuwannin.
Amma dokar hana tafiye tafiye tsakanin jihohi na nan za ta ci gaba da aiki, sai dai dokar bata shafi kayayyakin abinci da man fetir da sauran muhimman abubuwan bukata ba.
Sannan gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage dokar haramta zirga-zirgar jiragen sama tsakanin jihohi.
Kwamitin na shugaban ƙasa ya ce an buɗe zirga-zirgar jiragen sama tsakanin jihohi ne saboda sufurin jirgin sama na da tsari.
Dr. Sani Aliyu ya ce su ma jiragen an gindaya musu sharuɗɗan da za subi kafin suci gaba da harkoki daga ranar 21 ga watan Yuni.