Sabbin matakan sassuta dokar kulle a Najeriya

Sabbin matakan sassuta dokar kulle a Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta sanar da sabbin matakai na sassauta dokar kulle da aka kafa a ƙasar domin daƙile yaduwar cutar korona.
Daga cikin sabbin matakan da kwamitin shugaban ƙasa da ke yaƙi da annobar korona a Najeriya ya sanar sun haɗa da ɗage haramcin tarukan ibadah a Masallatai da coci coci.
Sassaucin na tsawon wata ɗaya ne da zai fara aiki daga ranar Talata biyu ga watan Yuni zuwa 29 ga Yuni.
 Sai dai shugaban kwamitin na shugaban ƙasa kuma sakataren gwamnatin Tarayya Boss Mustapha ya ce za a sake diba matakan idan wa’adin ya cika.
Sannan an sassauta dokar kulle ta mako huɗu da shugaba Buhari ya saka a Jihar Kano da zummar daƙile yaɗuwar cutar korona.
Shugaban kwamitin shugaban ƙasa mai yaƙi da korona, Boss Mustapha ne ya bayyana hakan a taron manema labarai a Abuja a yau Litinin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.