Akwai yi wuwar kara kwana daya domin bude kasuwanni a kano ya yinda Ganduje ya gana da manyan yan Kasuwa na Jihar Kano

Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya Jagoranci ganawa da Shugabanni da manyan yan Kasuwa na Jihar Kano don tattaunawa akan yadda za’a bi don daqile yaduwar cutar coronavirus a yayin bude Kasuwanni da Gwamnatin tabada dama ayi.

Cikin Jawabansu yan Kasuwar sun shirya raba safar rufe baki da hanci ga masu shiga kasuwannin su a wadannan ranakun dak ci gaba da bawa Gwamnati hadinkai don kaucewa Yaduwar cutar a Jihar Kano.
A Jawabinsa Mai Girma Gwamna yafara da jajantawa yan Kasuwar Jihar Kano bisa yadda mafi yawa suka tafka asara tare da addu’ar Allah ya yaye mana wannan annoba.
Sannan Gwamna yayi alkawarin duba yiwuwar kara ranakun bude kasuwannin idan aka ga yadda suka bi wadannan Dokoki da aka bayar.
Ganduje ya ce dukda cewa gwamnatin jiha bata da kudi, amma za subi dukkanin hanyoyin da suka kamata wajen taimakawa manyan da kana nan yan kasuwa wadanda sukafi galabaita a wannan yanayi, ta hanyar Sanya su cikin tsare tsare rage radadi da gwamnatin tarayya zata Samar anan gaba ta karkashin ma’aikatar kasuwanci.
Daga bisani ya umarci Kwamishinan muhalli daya hadakai da Shugabannin Kasuwannin domin ganin Gwamnatin ta qarawa kasuwannin kayayyaki irinsu Safa da kayan wanke hannu da kuma ci gaba da yin feshi a kasuwannin.
Gwamna yana tare da Mataimakinsa Dr Nasiru Yusuf Gawuna, Sakataren Gwamnati Alh Usman Alhaji, Kwamishinonin Yada Labarai dana Muhalli dakuma MDs na Kasuwannin Kwari, Singer, Sabongari.Yau,Talata.2/6/2020

Leave a Reply

Your email address will not be published.