Ganduje ya fitar da sabbin tsare tsaren bude kasuwanni a kano

Ganduje ya fitar ya fitar da sabbin tsare tsaren bude kasuwanni.

 A cikin bin umarnin gwamnatin tarayya na dakatar da dokar kulle da akayi don dakile yaduwar cutar Korona, Gwamnatin jihar Kano ta fitar da ka’idoji kan yadda jama’a za suyi game da damar zuwa kasuwanni da wuraren ayyukan tattalin arziki don gujewa hadarin ya duwar cutar acikin Jama’a.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ya ce bayan tattaunawa da manyan kwararrun ma’aikata kiwon lafiya da yin bita kan halin da ake ciki a Kano, yanzu haka an ba da izinin bude kasuwanni, wuraren ibada da Zirga-Zirgar mutane a ranakun Lahadi, Laraba da Juma’a daga 6:00 na safe zuwa 6:00 na yamma.
 
Ya ce gwamna Ganduje ya kira taron gaggawa tare da shugabannin kasuwanni kan yadda za a tabbatar da tsaurara matakan tsaro da ka’idojin kariya a kasuwanni da wuraren kasuwanci.
Bayanin ya kara jaddada cewa ya zama wajibi ga irin wadannan wuraren a tabbatar da bin ka’idojin kare Kai wadanda suka hada da tilasta yin amfani da takunkumin rufe fuska; samar da wuraren wankin hannu / tsaftace hannu; da kuma yawan gwada zafin jiki mai yawa akai-akai.
  
Kwamishinan ya yi nuni da cewa yayin da aka ɗage dokar kulle, dokar Hana Zirga-Zirga tsakanin Jihohi, tana nan, sai dai ban da hana shigo da kayayyakin amfani kamar kayan abinci, man fetur da kuma kayayakin aikin gona.
Ya ce yayin da makarantu za su kasance a rufe, kana an bukaci dalibai suyi amfani da damar karatu ta rediyo da darussan talabijin da gwamnatin jihar ke daukar nauyinsu
  
Kwamishinan ya kara da cewa  Ganduje ya danganta nasarar da ake samu na raguwar yawan masu kamuwa da cutar  da matakan da gwamnati da hukumomin kiwon lafiya ke dauka tare da bayar da muhimmanci ga yin addu’a da malamai da limamai ke yi da sauran mutanen jihar. Kuma ya yi kira da a yawaita irin wadannan addu’o’in har cutar ta shafe gaba daya.
Malam Garba ya kuma yabawa jama’ar jihar saboda hakurinsu da fahimtarsu a yayin da dokar ta hana su yin aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published.