Karfin GDP na Najeriya ya karu da 14% daga bangaren ICT -Isa Pantami

 

Karfin GDP na Najeriya ya karu da 14%   daga bangaren ICT–Isa Pantami

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Ibrahim Pantami ya ce bangaren ICT ya taimaka wajen bada gudumuwar 14.07% ga karfin tattalin arzikin Najeriya a farkon bana.
Dr. Isa Pantami ya ce ba a taba ganin irin wannan gudummuwa a alkaluman GDP na Najeriya ba a tarihi. Ministan ya bayyana wannan ta bakin hadiminsa, mista Femi Adeluyi.
A jawabin da ministan ya fitar ranar Lahadi a babban birnin tarayya Abuja, ya ce ya yi farin cikin jin labarin cewa bangaren kimiyya na ICT ya bunkasa tattalin arzikin kasar a 2020.
A cikin makon jiya ne hukumar NBS mai tattara alkaluma a Najeriya ta fitar da rahoton tattalin arzikin kasar na farkon shekarar nan da ake ciki, rahoton ya nuna GDP ya karu da 1.87%.
“Ya kamata a sani cewa bangaren ICT ya bawa GDP gudumuwar 14.07% a farkon 2020, wanda hakan ya zarce abin da aka samu na gudumuwar 13.32% a farkon shekarar da ta gabata.”
Ministan  ya sake cewa: “Ba a taba ganin irin wannan gudumuwa a tarihi ba.” Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya ce sun yi nasara ne a dalilin irin kokarin da gwamnatin Najeriya take yi.
Isa  Pantami ya bayyana wasu tsare-tsare da aka shigo dasu a karkashin shugabancin Muhammadu Buhari a matsayin abubuwan da suka taimaka wajen zaburar da bangaren.
A karshe, ministan tarayyar ya yi kira ga sauran bangarorin gwamnati suyi amfani da wannan dama da shugaba Buhari ya kawo wajen fadada amfanin da suke yi da kimiyyar na ICT.
Kamar yadda hukumar dillacin labarai ta rawaito, ministan yayi jawabin ta bakin Adeluyi.
 komawa ICT gadan-gadan zai bunkasa karfin tattalin arzikin kasar fiye da abin da aka gani a bana.
Jimillar tattalin arzikin Najeriya ya motsa ne da 9.5% ne a sakamakon gudumuwar da aka samu daga bangaren mai. Amma Kuma an  sami gudummuwar 90.5% daga sauran bangarorin na daban.

Leave a Reply

Your email address will not be published.