Majalisa ta amincewa Buhari ya karbo bashin Dala Bilyan $22.7bn

 

Majalisa ta amincewa Buhari ya karbo bashin Dala Bilyan $22.7bn

Majalisar wakilan tarayyar Najeriya ta amincewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, karbi bashin $22.7bn daga kasashen waje.
Yan majalisar sun amince da karbo bashin ne a zaman majalisan da ya gudana ranar Talata bayan samun rahoton kwamitin basussuka.
Idan Za ku iya tunawa lokacin da shugaba Buhari ya mika bukatar karban bashin a 2019, ya ce za’ayi amfani kudaden wajen wasu manyan ayyuka don jin dadin al’umma. TheCable ta hararo.
Amma wasu yan majalisa musamman daga yankin kudu maso Gabas (Kasar Igbo) sun nuna rashin amincewarsu da hakan inda sukaga yankinsu ba ta da rabo a ayyukan da za’ayi da kudin.
Hakan ya kai ga dakatad da lamarin bashin, sai yanzu aka samun daman cigaba bayan da Kakakin majalisan, Femi Gbajabiamila, ya roke su.
Gbajabiamila ya ce duk matakan da suka dauka na ganin cewa an magance matsalolin sun gamu da cikas saboda an riga an kammala yarjejeniya da wadanda zasu bada bashin.
“Saboda haka imma mu amince dashi gaba daya, ko kuma kada mu amince dashi gaba daya.” 
Kakakin ya kara da cewa majalisar ta samu nasarar yarjejeniya da fadar shugaban kasa cewa idan za’a karbi wani bashin Nan gaba, wajibi ne a sanya yankin kudu maso gabas da Arewa maso gabas ciki.
“A karon farko, mun ayyana ayyuka na musamman da za a yi. Mun yi yarjejeniya da bangaren zartarwa kan cewa wajibi ne a sanya wadannan ayyuka a wani sabon bashin da za a karba.” 
Shugaba Buhari ya mika bukatar karban bashi ne ga majalisar dokokin tarayya karkashin Bukola Saraki amma sukayi watsi da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.